Friday, February 1, 2019

Home › › AN KASHE WATA MATA TA HANYAR JEFATA A RIJIYA

Subscribe Our Channel



Masu aikin ceto sun gano gawar wata mata,
Shahida Bibi wacce a ke zargin 'yan uwanta maza
sun jefa ta cikin rijiya da ranta, sannan suka cike
rijiyar da kasa.
Mahaifiyar Shahida Bibi ce ta kai rahoton ga 'yan
sanda lamarin, inda ta ce 'ya'yan ta maza suna
yunkurin abin da suka bayyana da kawar da
shaidanu daga gidansu.
Ta ce wani mai bayar da maganin aljanu ne ya sa
su yin hakan.
'Yan sanda sun kama mazan biyu, 'yan uwan
matar
da ake zargi da kashe ta.
An ce mazan biyu sun nannade 'yar uwar ta su ne
a
cikin bargo, sannan suka jefa ta cikin rijiyar, suka
kuma cike rijiyar da kasa da duwatsu.
Masu aikin ceto sun shafe sa'o'i talatin suna
kokarin
ciro matar.
Masu aikin ceton sun rika hutawa saboda iskar
numfashi da ke kare musu.

No comments:
Write comments