Friday, January 25, 2019

Home › › Yadda ake Dora photo a wayar Android

Subscribe Our Channel


YADDA ZAKU DORA PHOTO AKAN
WAKA A WAYAR ANDROID .
Kamar yadda
kuke ganin wasu wakokin suna zuwa da
photo akansu sai muyi mamaki idan
mukaga hakan wato sai muga hotuna akan
wakoki to wannan aikine na computer,
to
amma yanzu zamuyi bayanin yadda zaka
dora photo akan waka batare da computer
ba kawai ta hanyar amfani da wayar
android .
Abin babu wuya kawai kuyi
download na wannan application mai suna .
Tcm music tag editor.apk .
Zaku iya
download dinsa a playe store ko a google
Bayan kayi download na wannan
application saika budeshi da zarar ka bude
zai kawoka inda wakokinsa suke to saika
duba folder da suke saika za6i wakar da
kake so ka sanyawa photo bayan ka zaba
nan take zai kawoka wani shafi inda ananne
zaka dora hoto Da sauran wasu gyare gyare
da zakayiwa wakar kamar su sauya .
Title===
Artist===
Album===
To idan zaka chanja ka lura
da kyau daga gefan kowane Rubutu akwai
inda aka Rubuta Fix to nan zaka danna sai
kayi edit ka rubuta abin da kakeso Sannan
daga kasa kuma zakaga photo da wakar
tazo dashi shima daga gefansa zaka zakaga
Fix saika danna nan nan take zata kawoka
gallary dinka saika za6i hoton da kakeso ka
dorawa wakar shikkenan da zarar ka xa6a
zai dawo dakai kan app din inda kake aikin
to saika duba sama zakaga inda aka Rubuta
SAVE AND CLOSE
shikkenan saika danna nan
domin yin save bayan ka gama saika fita
kaje ka duba wakar insha Allah zakaga
wannan hoton daka dora ya hau shikkenan.

No comments:
Write comments