Kamande yanda muka sani a yanzu kananan
wayoyi kirar kasar China sun bazu, kuma sunyi
yawa, komuce sun zama gama gari a hannun
al'umma. Wasu suna iya sarrafa application na
Java, wasu kuma basa iyawa. Watakila masu
amfani da irin wa'annan wayoyin zasuso sumori
Facebook, amma saboda babu wani application
na musamman da akayi saboda irin wa'annan
wayoyin yasa mutane basajin dadin wayoyin.
Wayoyin dazamuyi magana akai sune ake kira da
Chinese phone, wato wayoyin China, kamarsu
Tecno, da Gionee, da Itel, da Rokea, da MBO da
sauransu. Wa'annan wayoyin munsan wasu suna
zuwa da application na Facebook wasu kuma
basa zuwa dashi. Wasunsu kuma saide ayi
amfani da internet ayi Facebook, wanda hakan
abune mai wahala inde mutum bai kware a iya
sarrafa Facebook ba.
Koda waya mai Java ce idan aka tura mata
application na Facebook na Java, zaka samu
bata iya aiki dashi, kokuma bata iya tafiyar dashi,
saboda yayi mata nauyi. Wasu kuma
kwatakwatama basa iya installing nashi, saboda
banasu bane.
To acikin wannan tutorial din zamu baku wani link
ko URL address dazaku saukar da wani
application na Facebook, wanda yake kamada na
Nokia. Kuma shima yana aiki lafiya kalau, sannan
yanada saukin tafiyarwa a China phone.
Shimade wannan application din na Facebook ne,
kuma dai-dai yake dana Nokia, saide idan
katurawa Nokia bazata iya budeshi ba, kodayake
wasu Chinese phone dinma basa iya budeshi.
Yana aiki da data kuma yana sauri duk dacewa
wani lokacin yana dantsayawa, idan babu network
mai karfi.
Wannan application din yana aikine kadai gamasu
aiki da China phone, kuma bashida nauyi, domin
baifi 300Kb ba. Sannan ana iya installing nashi a
wasu wayoyin ko da kuwa babu memory card
idan akwai isasshen gurin ajiyewa.
Domin saukar da wannan application din kudanna
nan saiku saukar dashi a wayoyinku. Bayan
kungama saukarwa saikuyi installing nashi, saiku
fara more abunku. Kuma yana aiki sosai koda
kuna kan free mode ne. Amma fa asani baya aiki
sosai idan babu yanayin sadarwa mai kyau, kuma
mai karfi.
Bari de mutsaya anan inaga bayanin yakammalu,
kuma muna fatan zai taimaka wajen a more
Facebook a kanana dakuma wayoyin China.
Wannan tutorial din na jarrabashi nagani, kuma
yayi aiki sosai, na gwadashi akan wata Tecno.
Kucigaba da kasancewa da wannan shafin a
kodayaushe, domin hakan shine zaibamu kwarin
gwiwa wajen jajircewa dakawo muku ingantattun
tutorial, mun gode ahuta lafiya.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write comments