yadda ake bude sabon adireshin Email na
Gmail a wayar hannu. Da fatan duk wanda
ba shi da Email na Gmail, a yanzu ya
mallaki nasa. Idan kuma akwai mai
tambaya, ko kuma akwai wani abu da ba a
fahimta ba game da bayanin da muka yi,
to ana iya yin comment.
Yanzu kuma, za mu yi bayani ne a takaice,
kan yadda mai amfani da Gmail zai aika
sako daga Email din sa zuwa ga wani.
Wannan abu ne mai sauki da ba ya bukatar
wani dogon bayani.
Domin aika sakon Email daga Gmail din ka
kawai abin da za ka yi shi ne,
* Ka bude gmail din ka (wato ka yi login)
tare da email din ka da password ta shafin
www.gmail.com .
* Idan ya bude sai ka nemi inda aka sa
'Compose' sai ka danna.
* Zai budo maka wani shafi.
* To, a wajen da ka ga an sa 'To' anan ne
za ka rubuta adireshin Email din wanda za
ka aika ma sakon.
* Wajen da aka sa 'Subject' kuma a nan ne
za ka rubuta 'maudu'in sakon'.
* Sai ka yi kasa, ka rubuta wasikar ka a
akwatin da aka tanadar, wato wajen da aka
sa 'Message'.
* Da ka gama sai ka danna 'SEND'.
Shikenan! Nan take sakon zai tafi zuwa
Inbox din wanda ka aika ma.
No comments:
Write comments